ABNA24 : Rundunar sojin kasar Faransa ta sanar da cewa, wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da bama-bamai a cikin wata mota, a lokacin da sojojin Faransa suke gittawa a cikin motoci masu sulke a yankin Goussi da ke tsakiyar kasar mali, inda 6 daga cikin sojojin suka samu raunukua, gami da wasu fararen hula 4. Wadanda suka ganewa idanunsu abin da ya faru sun sheda cewa, bayan faruwar lamarin wasu sojojin kasar ta Faransa sun iso wurin cikin gaggawa domin kawo dauki, sun kuma dauki wasu 3 daga cikin sojojin da suka samu raunuka a cikin jirgi mai saukar angulu zuwa yankin Gao. Wannan dai na zuwa nea daidai lokacin da Faransa ke kokarin rage yawan sojojinta daga yankunan Kidal da Tinbuktu zuwa yankunan da ke kan iyakokin kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar.
342/